1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta hana fararen hula tsere wa rikici

Ramatu Garba Baba MNA
February 18, 2019

Mayakan IS a Siriya sun tare hanya daya tilo da jama'a ke bi don guje wa rikici. Kakakin kungiyar mayakan Syrian Democratic Forces da Amirka ke jagoranta ya sheda cewa, dubban jama'a sun rasa yadda za su yi.

https://p.dw.com/p/3DYab
Syrien Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/C. McGrath

Mayakan sun kange garin don hana ma jama'a da ke yunkurin ficewa hanya, sun kuma yi garkuwa da wasu daruruwan jama'a. Kakakin kungiyar Syrian Democratic Forces ya kara da cewa, sun yi hakan ne a matsayin kare kansu, ganin aski ya zo gaban goshi a kokarin da ake na ganin bayansu.

A watan Disambar bara, mutum fiye da dubu arba'in ne suka yi amfani da wannan kafar don tserewa daga kauyen da ke a yankin Deir el-Zour a yayin wani gumurzu a tsakanin bangarorin biyu.

Daruruwan mayakan na IS a Siriya sun mayar da wannan yankin tungarsu, ya kuma kasance wuri na karshe da ya yi saura a karkashin ikonsu.