Matsayin Ngozi a kan cin hanci a Najeriya | Labarai | DW | 13.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsayin Ngozi a kan cin hanci a Najeriya

Ministar kudin tarayyar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta ce dole ne shugaban kasa ya yi wa fannin hako man fetur gyaran fuska idan ana so kasar a ta rabu da cin hanci.

Ministar kudin Tarayyar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta bukaci shugaba Goodluck Jonathan ya yi gyara-gyaren da suka wajaba domin kawo karshen ja'ibar cin hanci da karbar rashawa da ke shafa wa kasar kashin kaji. Cikin wata kasida da ta rubuta, aka kuma wallafa a mujallar Financial Times, Ngozi-Iweala ta ce dole ne shugaba Jonathan ya kafa kwamiti da zai gudanar da bincike dangane da zargin sama da fadi da dukiyar kasa da aka yi a kamfanin mai na kasa wato NNPC.

Wannan kasidar Ngozi-Iweala ta zo ne makwanni kalilan bayan da tsohon shugaban babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya ambata cewa an karkata dubban miliyoyin daloli na man fetur a NNPC. Lamarin da ya janyo masa bakin jini tsakanin wadanda ke rike da madafun iko, inda aka dakatar da shi watannin kalilan kafin kammala wa'adinsa.

Cin hanci da karbar rashawa dai ya yi katutu a fannin hakar danyen man fetur da kuma sayar da shi a Najeriya, kasar da ta fi kowace hako danyen wannan arziki na karkashin kasa a nahiyar Afirka.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal