Matsayin alkalan Najeriya kan kame takwarorinsu | BATUTUWA | DW | 11.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Matsayin alkalan Najeriya kan kame takwarorinsu

A ci gaba da kokarin neman mafita a rikicin kamen alkalai da ke raba kan al'ummar Najeriya, majalisar koli ta alkalan kasar ta yi zaman gaggawa a Abuja da nufin yanke hukuncin karshe kan batun, inda ta nuna bacin ranta.

Jami'an tsaro sun hana masu farautar labarai matsawa wurin har sai an kamalla taron da ake yi wa kallon mai tasiri a kokarin ci gaba da dambarwar da ta yi nisa wajen raba kan al'ummar tarayyar Najeriya. Su kansu majalisun tarrayar kasar guda biyu sun bi sahu tare da 'yan majalisar wakilai wajen neman bayyanar shugaban hukumar DSS a gabanta domin jin dalilan sumamen da ya tada hankula.

Duk da cewar 'yan uwansu na dattawa sun kauce wa kokarin jin baki na shugaba na jami'an tsaron, ra'ayi ya kusan zama daya a tsakanin 'ya'yan dattawa na nuna bacin ransu bisa matakin da a cewar Senata Joshua Lidani da ke zaman dattijo daga Gombe ya saba ka'ida

Bayanan da ke kara fitowa fili daga hannun jami'an hukumar DSS  na nuna adawa  ta majalisar alkalan game da mika wasu a cikin 'ya'yanta da ake zargi da sana'ar cin han

ci a maimakon adalci a  cikin sunan alkalanci. So kusan tara ne DSS suka ce sun gayyaci alkalan kafin yanke hukunci na samamen. 

 Sai dai kuma a wani abin da ke nuna alamar ko in kula, tuni dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aike da sunayen  wasu alkalai  guda biyu  Mai shari'a Sidi Bage daga Arewa taTtsakiya da kuma mai shari'a  Paul Jauro daga Arewa maso Gabas domin amincewa da nadinsu zuwa manyan alkalai a cikin kotun kolin Najeriya.

Koma wane irin matsayi ne dai majalisar take iya dauka, ya zuwa karshen taron da ya dauki awoyi sama da bakwai sannan kuma ke gudana a farfajiyar kotun kolin dai, a tunanin Barrister Buhari Yusuf da ke zaman wani lauya mai zaman kansa a nan a Abuja ba shi da tasiri wajen hana alkalan fuskantar kuliya cikin shari'ar da ke zaman tsumangiyar kan hanya da ta fyadi sojoji da masu siyasa yanzu haka kuma ta gangaro kan alkalai

 

Sauti da bidiyo akan labarin