Matsalolin tsaro na neman gagarar kundila a Najeriya | Zamantakewa | DW | 20.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalolin tsaro na neman gagarar kundila a Najeriya

A Najeriya matsalolin tsaro na kara kamari a yankunan da dama, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke ci gaba da yin tsayuwar gwamin jaki a game da bukatar 'yan majalisu da ma wasu 'yan kasar kan sauya hafsoshin soja.

A Najeriya matsalolin tsaro na kara kamari a yankunan da dama na kasar musamman na yankin arewacin kasar inda 'yan Boko Haram da kuma 'yan bindiga ke ci gaba da daukar rayukan jama'a. Sai dai kuma duk da kamari da yanayin tabarbarewar tsaron ke yi, gwamnatin kasar ta ce ba ta da niyyar sauya hafsoshin sojan kasar, wannan kuwa duk da kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar da kuma musamman 'yan majalisa ke yi na ganin an sauya hafoshin tsaron kasar domin dora sabbin jini da za su fi tunkarar matsalolin na tsaro a fadin kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin