1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matafiya kan fuskanci matsaloli a Afirka ta Yamma

October 27, 2021

‘Yan Kasashen Afirka ta Yamma da sauran kasashen da ke tafiye-tafiye a tsakanin kasashen Afirka ta Yamma a motoci sun bayyana yadda suke shiga kunchi a wasu kan iyakokin kasashen da su ka ratsa.

https://p.dw.com/p/42Eyd
Symbolbild | ECOWAS | Westafrikanischer Regionalblock verabschiedet neuen Plan zur Einführung einer einheitlichen Währung im Jahr 2027
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

 

Wannan dai haifar da tambayoyin na tasirin shige da ficen kasashen da suka amince a yi zirga-zirga ba tare da takardar izinin shiga kasa da ake kira visa ba tsakanin kasashe da ke cikin Kungiyar ECOWAS.

Manufar shige da fice marar shinge da kasashen yammacin nahiyar Afirka su ka cimma yarjejeniyar samar tsakanin kasashen ECOWAS shi ne habaka kasuwanci da zamunta domin karfafa tattalin arzikin kasa na wadan nan kasashe da ke cikin kungiyar

Grenze Nigeria Benin
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

To sai a iya cewa Haka ba ta cimma ruwa ba don kuwa matafiya na samun tarnaki tsakanin kasashen saboda zargin cin hanci da ake zargin ana samun tsakanin jami'an da ke kula da shige da fice da kuma na Kwastam har ma da jami'an Soji da ‘Yan Sanda da ke kada shingen bincike a yawancin hanyoyin.  

Wasu matafiya a wadan hanyoyin da na tattauana da su sun bayyana min cewa an karbi kudade daga hannun su a irin wadan wurare da sunan biyan kudin shiga kasa da ya kama daga Jaka 10 ko kuma Naira dubu 10 ko kasa da haka ko ma fiye a wasu wurare.

Da farko na jin ta bakin Malam Hidir Ahmad Musa dan jihar Kano a Najeriya wanda kuma shafe shekaru ya bin hanyoyin tsakanin kasashen yammacin nahiyar Afirka ya ce suna ganin matsaloli na karbar cin hanci tsakani jami'an da ke kula da iyakokin kasashen.

Nigeria Seme Grenze zu Benin
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A matsalolin da ake gamuwa da su ba a ware mata domin kuwa Sayyada Rabi Bababa daga jihar Gombe a Najeriya ta ganin sai mahukuntan sun tashi tsaye domin magance matsalolin.

Harkokin kasuwanci na shiga mawuyacin hali tsakanin kasashen musamman ganin yadda ‘yan kasashen ke fama da biyan kudade na ba gaira ba dalili a hanyoyin da suke bi.

Ko me ya kamata a yi amgance wannan matsalar Malam Usman wanda aka fi sani da Ladan daga Niamey a jamhuriyar Nijar ya bani amsar wannan tambaya.

Masana da masharhanta na bayyana fargabar wannan matsala da ake za iya samun sauki safarar haramtattun makamai da kuma ruruwan wurar rikicin matsalolion tsaro saboda an fi kulawa da karbar kudi maimakon abun da mutum yake wucewa da shi.