1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar sharar leda ta zame wa al’umma alakakai

Umar Zahradeen YB
June 6, 2019

Ranar biyar ga watan Yuni ake bikin ranar muhalli a sassa daban-daban na duniya. Sharar leda dai ta zama alakakai ga misali a jihar Kadunan Najeriya.

https://p.dw.com/p/3JsRH
Indonesien - Zulieferung von Ecoton bezüglich Australischer Müll in Ost-Jawa
Irin wannan shara dai ta zama tashin hankali anan ma IndonesiyaHoto: Prigi/Ecoton

Bayan da waikilin DW Zahraddeen Umar Dutsen Kura ya leka shagon Malam Idris da ke a unguwar Tudun Wada Kaduna, ya gano a kowace rana wannan shago kan bayar da akalla  leda guda dari daya ga kwastomominsa don su sanya kayan da suka saya. Malam Idris ya ce ya taba jarraba takaita ya bayar da leda amma kuma sai hakan ya korar masa kwastoma: "Wani kostomana rigimi muka yi da shi kan batun na leda."

To sai dai ga Habiba Ibrahim mai sayar da Ganda da ganyen ogu da sauran kayan miya a kasuwar Barci Kaduna, ita ba ta taba yin sa-in-sa da kwastoma akan leda ba. Amma kuma tana kashe kudi sosai wurin biya wa masu siyan kayanta bukatarsu: “Ina kashe kudade da yawa kafin na sayar da kayan saboda sawa a cikin leda."

Tanzania Dar es Salaam - Plastikverbot
Masu shago dai na siyar da kaya a ledar kamar nan a birnin Dar es SalaamHoto: DW/S. Khamis

Da alama dai akulli yaumin bukatar leda karuwa take. Adamu Mudi, wani magidanci, ya shaida wa DW cewa ba zai iya yin sayayya ba tare da an sanya masa leda ba saboda sirrinta abin da ya saya.

"Kamar wannan leda idan na gama aiki da ita ina sata a kwandon shara, wata kuma na sake amfani da ita, akwai dai sirri."

Irin yadda ake jefar da ledoji a wurare daban-daban masana irinsu Dr. Yusuf Sale na jami‘ar jihar Kaduna na cewa akwai illa matuka domin leda na dauke da wasu sinadarai masu lahani ga dan Adam:

“Leda kan haifar da matsala ga muhalli idan ma ta ragargaje a kasa ta kan shiga kasa ta haifar da illa ga dan Adam.“

A cewar masana sinadaran da ke tattare da leda a wasu lokuta har cutar daji ma suke sababawa. To sai dai da alama wannan ba zai sauya ra'ayin Hamisu kudan ba wanda ya ce ya sani da haka amma yana matukar bukatar ta ledar a harkokinsa.

A watan da ya gabata ‘yan majalisar dokokin Najeriya sun zartar da kudurin da zai takaita amfani da ledar, kuma masu fafutukar kare muhalli na son ganin gwamnatin Najeriya a wannan sabon zangon nata ta magance matsalolin da leda ke haifarwa ga mutum da duniyarsa.