1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Matsalar hana 'yancin fadin albarkacin baki

June 9, 2023

Kafofin sada zumunta na wannan zamani na cin karo da turjiya daga shugabannin da ke rike da mukaman mulki a kasashen Afirka, saboda toshe damar caccakar su da galibi ake yi ta kafofin.

https://p.dw.com/p/4SNhZ
Matsalar hana fadin albarkacin baki a shafukan sada zumunta na zamani a Afirka
Matsalar hana fadin albarkacin baki a shafukan sada zumunta na zamani a AfirkaHoto: Adobe Stock

Shugabannin kasashen Afirka na daga cikin shugabannin da ke hana 'yan kasashensu 'yancin bayyana wasu ra'ayoyi ko suka ta shafukan sada zumunta na zamani a lokutan da suka lura cewa abubuwan da shafukan ke dauke da su sun ci karo da manufofinsu. Hakan na faruwa ne duk da cewa tsarin dimukuradiyya da suke a bisa doronsa ya yarda da bai wa jama'a ‘yancin fadar albarkacin baki.

Tabbas kafofin zumunta na wannan zamani da suka zama ruwan dare, na cin karo da turjiya daga shugabannin da ke rike da mukaman mulki a kasashen Afirka, saboda toshe damar caccakar su da galibi ake yi ta kafofin. Shugabannnin a gefe guda kuwa na cin moriyar kafafen ta hanyar yada farfagandar da ba lallai ne su kasance gaskiya ba a wani kaulin.

Shugaban kasar Yuganda Yoweri Musevini
Shugaban kasar Yuganda Yoweri Musevini Hoto: ABUBAKER LUBOWA/REUTERS

Alal misali, a shekara ta 2021 kamfanonin Facebook da Twitter sun soke kusan shafuka 440, da ke da alaka da jam'iyyar gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni na  na Yuganda, saboda zargin su da yada farfaganda, ko ma wasu bayanan da ke kokarin sauya tunanin da suka shafi ra'ayoyin al'uma na zahiri da kuma yi wa ‘yan adawa barazana.

A cewar Nicholas Opiyo, gwamnatocin na Afirka kan yi amfani har ila yau da wasu manhajojin kwanfuta da musamman aka tsara su domin yada manufofin shugabanni, baya ga wadanda ake bajewa a kan shafukan zumunta. Kamfanin Twitter ya ma soke wasu shafukan a kasashe irin su Najeriya da Tanzaniya a baya.

An taba dakatar da kamfanin Twitter a Najeriya
An taba dakatar da kamfanin Twitter a NajeriyaHoto: CONSTANZA HEVIA/AFP

Idan kuma za a iya tunawa, tsohuwar gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ma ta dakatar da shafin Twitter a baki dayan kasar, saboda wasu kalaman da suka ci karo da ra'ayin gwamnatin, matakin da ake ganin wasu shugabannin Afirka ma kan dauki fiye da su. Ana dai amfani da wadannan shafuka na sada zumunta sosai a lokutan da siyasa ke zafi a kasashen duniya, inda a wasu lokutan ake samun tashe-tashen hankula bayan yada labaran karya a nahiyar. Hakan na sa shugabannin toshe shafukan.

Kamar yadda cibiyar nazarin harkokin kasashe a Afirka ta Kudu, toshe kafofin sadarwar Intanet ko ma kama masu sukar lamirin gwamnati a kasashen Afirka bakar fata, abu ne da ke ci gaba da nuna yadda tsarin gudanar da mulki irin na kama-karya ke ci gaba da karfi a nahiyar. A karshe dai dan gwagwarmaya na kasar Yuganda Nicholas Opiyo, na fatan masu ta'ammali da shafukan na sada zumunta, za su gane cewa, ba duk wani abun da suka gani a shafukan ne ke zama labari na hakika ba.