1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar garkuwa da mutane a arewacin Kamaru

February 11, 2022

Garkuwa da mutane a yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru da ke amfani da turancin Ingilishi da ke fama da rigimar ‘yan aware na dada karuwa.

https://p.dw.com/p/46uCC
'Yan awaren Kamaru a wajen binciken ababen hawa
'Yan awaren Kamaru a wajen binciken ababen hawa Hoto: Adrian Kriesch/DW

 A ‘yan kwanakin da suka gabata ne dai aka yi nasarar hada wasu ma’aikatan wata gonar roba da aka sace da iyalansu, bayan wadanda suka yi garkuwa da su, sun zarge su da hada baki da sojojin gwamnatin Kamaru. Har yanzu dai akwai wasu jami’an gwamnati da wani basaraken da aka yi garkuwa da su a yankin. 

Iyalai da dangi da ma sauran al’uma ne suka taru a garin Tiko da ke yankin kudu maso yammacin kasar Kamaru, inda suke nuna godiyarsu ga Allah da ya kare rayuwar ma’aikatan gonar roba da aka sako bayan kwashe kwanaki 10 a hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

Kamerun Justiz l Festnahme im Zusammenhang mit anglophone Krise
Wasu mutane da aka kama a yankin Ingilishi na KamaruHoto: STRINGER/AFP/Getty Images

Cikin wani faifen bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, ana iya ganin mutanen su takwas a gajiye cikin yanayi na rashin koshi, inda mutane ke mika musu ruwan sha. Gabriel Nbene Vefonge, shugaban gamayyar kungiyar manoma a Kamaru, na daga cikin wadanda ke hakurkurtar da mutanen da aka sako.

IYalansu baki daya sun shiga wani mumunan yanayi, inda in banda addu’o’I babu wani abin da suka iya yi. Fatansu shi ne kada Allah Ya sa su sake ganin haka. Wadannan da kuke gani, su ne ke dauke da nauyin iyalansu. Yayin dai da suke sake tozali da ‘yan uwansu, babu abin da za mu ce sai godiyar Allah da gano kansu da suka yi." 

Kamerun Mitglieder der Gendarmerie
Wasu sojojin Kamaru cikin shirin ko ta kwanaHoto: Marco Longari/AFP/Getty Images

Yayin da wadannan ke farin cikin sako musu ‘yan uwa da aka yi, a gefe guda kuwa, har yanzu ba a san inda wasu jami’an gwamnati ba da ma wani fitaccen basarake da aka sace a arewa maso yammacin kasar suke ba, watanni bayan yin awon gaba da su. Cikin watan Yunin 2021 ne dai, aka sace jami’an gwamnati su shida a yankin Ndian na kudancin Kamarun. 

Bayan gano wani guda a mace ‘yan awaren yankin sun dauki alhakin kashe shi, inda suka zarge shi da hada kai da mahukuntan birnin Yaounde. Daga nan kuma babu wani labarin sauran mutanen biyar.

Haka ma babu labarin basarake Fon Kevin Shumitang. Shi ne dai babban jagoran majalisar sarakunan gargajiyar yankin arewa maso yammacin Kamarun, wadda ke kula da ci gaban al’umomin shiyyar. Gwamnatin kasar ta ce an sace Fon Kevin Shumitang ne daga fadarsa da ke a Bambalang cikin watan Disambar bara. Fru Angwafor, shugaban majalisar yankin arewa maso yamma, ya ce shi dai yanzu ya mika wa sojoji wannan batu na neman sakin basaraken.