Matashiya mai tallafawa ′yan gudun hijira | Himma dai Matasa | DW | 03.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashiya mai tallafawa 'yan gudun hijira

A Katsina wata 'yar jaridan gidan Television ta sadaukar da kanta wajen bullo da wasu shirye-shirye dan fadakar da mutanen jihar, mahimmancin tallafa ma 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya koro daga jihar Barno


Dalilin wannan shirye shirye dai yasa yanzu yan gudun hjira a jihar Katsina suna samu kulawa sosai kama daga biyan kudin haya da abinci da samar masu sana'o'i da kuma ilimin yayansu kyauta. Wannan yar jarida dai Hauwa'u Ibrahim Jikamashi, ta bayyana cewa a lokacin wata ziyara da ta kai daya daga cikin gidajen 'yan gudun hijirar ta ga halin da suke ciki yaja hankalinta na daura damarar bada gudummuwar ta garesu kamar yadda ta shaida wa DW. 

"Da farko dai abun da ya fara jan hankalina muna magana da wata take fada mun cewa Katsina akwai 'yan gudun hijira, to lokacin sai na same ta mukaje gurinsu mukaga halin da suke ciki, wanda a wannan lokacin na yi amfani da dama ta a matsayina na yar jarida na ga irin mawuyacin halin da suke ciki na matsalar abinci da sutura da wurin zama. To a lokacin ne na rubuta wani rahoto na musamman akan halin da suke ciki a jihar katsina " 

To hada wannan rahota na musamman da wannan 'yar jarida ta yi ya sa ta dau hanyar samun nasarar abun da take nema dangane da kokarinta na tallafama 'yan gudun hijirar. Inda Hawa'u ta ce.

"Bayan na yi wannan rahotan sai mutane suka rika zuwa suna nema na akan rahotan, suna tambaya shin dama Katsina akwai yan gudun hijira? Haka dai muka cigaba da tallafa masu da abubuwa iri daban-daban, kama daga abinci zuwa sutura da kuma sama masu wurin zama" 

Baya ga wannan shiryeshirye, Hauwa'u ta kan bi masu hannu da shuni da kanta ta nemar wa 'yan gudun hijiran taimako kuma ta kan yi amfani da kudadenta wajen taimaka masu.

"To sai na yi amfani da damata, akwai mutanen da nike hulda da su musamman akwai uwar gidan Gwamnan jihar Katsina Hajiya Hadiza Aminu Bello Masari lokacin na je na gaya mata ga halin da 'yan gudun hijira suke ciki a jihar Katsina, basu da wurin zama da abinci, to a lokacin ne ta bani kudi na je na samar masu gida da kuma abinci" 

To bayan nan wakilin DW Yusuf Ibrahim Jargaba, ya ji ta bakin wadan nan yan judun hijira, wadanda suka je jihar Katsina daga karamar hukumar Bama ta jihar Barno, inda suka tabbatar da irin gagarumar gudummuwar da take basu 

"Gaskiya ta yi mana kokari ta sa an bamu buhunan shinkafa da masara da hatsi da kuma kudi masu yawa" 
"Sunana Hauwa gaskiya kokarin da Hauwa'u tai mana sai dai muce Allah ya saka mata da alkairi