Matashi mai sana'ar gidajen kifi na zamani a Najeriya
December 19, 2018Talla
Shi dai wannan matashi mai cikakken suna Abdul-rauf Mansur Babangida dama dai tuni ya kammala digirinsa a fannin kiwon kifi a jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato, ya ce ya yanke shawarar rungumar harakar kifin ne gadan-gadan sakamakon rashin aikin yi da ya tsinci kansa a ciki. Yanzu haka dai wannan matashi ya kawo wani sabon abu da bakasafai aka saba ganinsa ba a birnin na Sakkwato na samar da nau’ukan kifi kama daga na kallo da kuma mai cin dattin kafa. Ko da yake bayan shafe tsawon shekaru matashin na gudanar da wannan sana’a, da sanadin hakan ya kai shi ga bude kamfani mallakarsa, mai suna DR. Fish Spa Aquarium. Duba ga yadda matashin ta kaishi ga bude rassa na wannan kamfani a wasu sassan biranen kasar.