Matashi mai koya wa mata girki | Himma dai Matasa | DW | 13.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashi mai koya wa mata girki

Wani matasahi a Jihar Kano da ke Najeriya da ya nakalci girke-girke, yanzu haka ya na koya wa mata girke-girke da koya musu tsaftar jiki da ta abinci mai gina jiki.

Shi dai wannan matashi mai suna Bashir Bello wanda ake yi lakabi da ''Dan Shila'' tun ya na karami ya ke da sha'awar girke-girke wanda ba kasafai mazan kan yi ba musamman ma dai a arewacin Najeriya. Bashir ya ce irin kalubalen da ake fuskanta na rashin iya girkin wasu matan musamman ma matasa ne ya sanya shi fara wannan aikin.

Matashin ya ce daga kafafen watsa labarai ya fara musamman ma rediyo inda ya ke gabatar da shiri na musamman da ke koya girki kuma kyauta ya ke yin wannan harka ba wai kudi ake biyansa. Baya ga batun koya girki, matashin har wa yau na koyawa mata yadda za su sarrafa abinci mai gina jiki kana ya na koyawa mata irin matakan da za su bi wajen yin gyaran jiki. Tuni dai mata da dama suka ce sun amfana da wannan tsari.