Matashi mai fafutukar yaki da shan miyyagun kwayoyi | Himma dai Matasa | DW | 14.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashi mai fafutukar yaki da shan miyyagun kwayoyi

A jihar Filato ta Najeriya matasa da dama da ke shiga harkar shaye-shaye na miyyagun kwayoyi sun soma barin wannan muguwar sana'a sakamakon tallafin da suke samu daga wani matashi mai suna Abubakar Sani Abdul.

Abdubakar Sani Abdu wanda shi ma matashi ne ya ce babban burinsa shi ne taimaka wa dimbin matasa wadanda ya tabbatar babu yadda za su yi su taimaka wa rayuwar kansu, don haka yake iyaka yinsa na ganin suna rayuwa ta kwarai. Wannan shi ne abin da ya sa ya shiga wannan aiki na taimaka wa rayuwar matasan

Wannan matashi dan fafutukar dai tuni har ya kafa wata cibiyar tsugunar da matasa, kuma ya shaida wa wakilin DW cewar yakan yi bincike don gano inda matasan kan zauna su yi shaye-shaye, sa'anan sai ya tinkaresu da sunan zai yi abota da su kafin kuma a bisani sai ya bayyana manufarsa.

Sauti da bidiyo akan labarin