1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hana fitar da shinkafa daga Indiya ya shafi Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe SB)(USU
October 12, 2022

Kasashe musamman na Afirka suna jin radadin matakin gwamnatin kasar Indiya na hana fitar da shinkafa daga kasar zuwa kasashen ketere.

https://p.dw.com/p/4I58n
Hoto | Indiya | Gona
GonaHoto: Dar Yasin/AP/picture alliance

Kasashen Afirka na ci gaba da radadin matakin da Indiya ta dauka na hana fitar da shinkafa zuwa waje sakamakon fari da ya shafi yankunanta da ake nomawa. A halin yanzu dai, Senegal da Côte d'Ivoire da kuma Jamhuriyar Benin da ke shigo da wani kaso mai yawa na shinkafarsu daga Indiya na cikin jerin kasashen da ke fuskantar karancin wannan abinci.

Wannan matakin takaita fitar da hatsi da Indiya ta dauka ya shafi nau'in shinkafa da kasar Senegal ke shigowa da shi da yawa. Daga shekara ta 2021 zuwa 2022 kawai, Senegal ta shigo da tan miliyan daya na shinkafa daga Indiya, lamarin ke nuna yawan dogaro da wannan kasa ke yi wajen samun hatsin da take bukata.

Fari | Trinidad
FariHoto: robertharding/picture alliance

Ita dai fadar mulki ta New Delhi ta dauki wannan matakin takaita fitar da hatsinta ne bayan da yankunan da ake noman shinkafa suka fara fuskantar babban fari. Amma dai Indiyar ta sanar da kasashen Afirka da abin ya shafa tun cikin watan Mayun da ya gabata. Sai dai tun daga lokacin zuwa yanzu ba su sami mafita ba, kamar yadda Momath Cissé, mataimakin shugaban kungiyar Senegal da ke kare masu amfani da kayayyaki ya bayyana.

Ita kuwa kasar Jamhuriyar Benin tana shigo da kashi 75% na shinkafar da ake ci a kasar daga Indiya. Sai dai inda gizo ke saka shi ne, ana karkatar da wani bangare na hatsin da ake shigo da su ba bisa ka'ida ba zuwa Najeriya da Burkina Faso.

Amma Honorat Satoguina, masanin tattalin arziki a Jamhuriyar Benin ya ce matakin da New Delhi ta sanar, zai tilasta wa kasarsa canza wasu halaye tare da tilasta wa 'yan kasar Benin rage yawan amfani da shinkafa a matsayin abincin yau da kullum.

Amma sakamakon barazanar karancin hatsi da wasu kasashen yammacin ta Afirka ke fama da ita, ya sa Momath Cissé na ganin cewa dole ne a canza dabarun noma na Senegal idan ana son shawo kan matsalar.

Su ma sauran kasashe kamar Côte d'Ivoire da ke shigo da shinkafa daga waje, ya zama tilas a gare su da su rubanya abin da suke nomawa a gida idan suna son kauce wa karancin hantsi. A halin yanzu dai, kasar na samar da tan miliyan daya na shinkafa a kowace shekara, amma don gamsar da masu amfani da ita, Côte d'Ivoire na bukatar shigo da karin kimanin tan guda daga waje.