1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsadar hada kayan aure a Adamawa

March 23, 2020

Ganin yadda tsadar aure ke hana matasa yin aure a jihar Adamawa majalisar Koli ta addinin musulunci a jihar ta fito da wasu ka'idoji na yadda za a saukake yin aure.

https://p.dw.com/p/3ZW8G
Nigeria | Nigerianische Nationalmoschee
Hoto: Imago Images/F. Stark

Najeriya dai na daga cikin wasu kasashe da wasu na ganin su fama da matsalar tsadan aure a nahiyar mu ta Afrika, inda samaki da ‘yan mata da dama ke zaune babu aure. Wannan dalilin yasa majalisar koli ta addinin musulunci a jihar Adamawa ta fito da wasu ka'idoji na yadda za'a saukake yin auren.