1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Masar za ta maka Isra'ila a kotun ICC

Binta Aliyu Zurmi
May 12, 2024

Kasar Masar ta sanar da cewa za ta mara wa kasar Afirka ta Kudu baya a hukumance, na kalubalantar Isra'ila a kotun ICC kan zargin kisan kare dangi da take yi wa Falasdinawa a Gaza.

https://p.dw.com/p/4flRh
Prüfung Israels Besatzungspolitik am Internationalen Gerichtshof in Den Haag
Hoto: Selman Aksunger/AA/picture alliance

A sanarwa da ma'ikatar harkokin wajen Masar ta fitar, ta ce ta dauki wannan matakin garzayawa kotun ICC ne duba da yadda harin da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa a Gaza ke hallaka fararen hula da basu ji ba su gani ba.

Sanarwar Masar ta kara da cewa Isra'ila na ci gaba da kai harinta ne a kan fararen hula da ma lalata ababen more rayuwa a Zirin.

Masar na daga cikin kasashen da ke fadi tashin ganin an cimma yarjejeniyar kawo karshen wannan yaki a tsakanin Isra'ila da Hamas.