Masar ta garkame wasu fitattun mata ′yan fafutuka | Labarai | DW | 18.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Masar ta kama mata 'yan fafutuka

Masar ta garkame wasu fitattun mata 'yan fafutuka

Iyayen matan da aka kama din sun ce an kama 'ya'yansu saboda sun bukaci hukumomin kasar su saki wasu 'yan gidan yari ganin yadda cutar Coronavirus ke ci gaba da yaduwa.

Matan da aka kama din dai sun hada da Mona da Laila da Ahdaf da kuma Rabab, dukkaninsu sun yi fice a kasar Masar a wurin fafutukar kare hakkin jama'a. An kama matan bayan sun yi wata 'yar zanga-zanga a birnin Alkahira a gaban wani ginin gwamnati. 

Rahotanni sun nuna yadda 'yan matan suka yi bidiyo na kai tsaye-facebook live- inda suka ce sun zo wurin ne don kira ga hukumomi da su saki mutanen da ke gidan kaso domin kowa ya san cewa gidajen yari na Masar sun zama tamkar wurin kamuwa da cututtuka. Sai dai kafin su kammala wannan facebook live din jami'an tsaro suka karbe wayar da suke daukar bidiyon da ita kuma suka yi awon gaba da su.