Masar: Hallaka shugaban tsagerun Sinai | Labarai | DW | 05.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar: Hallaka shugaban tsagerun Sinai

Dakarun yaki da ta'addanci na kasar Masar sun sanar da cewa sun hallaka jagoran kungiyar tsagerun yankin Sinai da ke da alaka da kungiyar IS Abu Dua al-Ansari.

Dakarun yaki da ta'addanci a yanki Sinai na Masar

Dakarun yaki da ta'addanci a yanki Sinai na Masar

A cewar rundunar sojojin Masar din, sun hallaka al-Ansari ne tare da wasu 'yan ta'adda 45, yayin wasu jerin hare-hare da suka kai a maboyar 'yan ta'addan da ke kusa da Arish babban birnin gundumar arewacin Sinai din, kana kuma sun raunata wasu 'yan ta'adda 20. Sai dai har kawo yanzu babu tabbaci kan lokacin da dakarun yaki da ta'addancin na Masar suka kai hare-haren a yankin na Sinai da ke fama da ayyukan 'yan ta'adda.