1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin sakin tsaffin gwamnonin Najeriya

Abdullahi Maidawa Kurgwi
August 9, 2022

A Najeriya musamman a jihohi biyu na Filato da Taraba ana ci gaba da samun ra'ayoyi masu saba wa juna kan sakin tsaffin gwamnonin jihohin da aka samu da laifin cin hanci.

https://p.dw.com/p/4FKEb
Öl Globaler Einfluss Geld Finanzen Nigeria Naira
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Bayan sakin tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye  daga gidan yari, jama'ar Filato na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabanbanta  dangane da sakin tsohon gwamnan wanda ake zargi da laifin sace kudin jama'ar  lokacin da yake kujerar  gwamnan jihar.

Tun dai a ranar 14th, ga watan Afrilu na wannan shekarar ce majalisar koli ta tarayyar Najeriya ta yi ahuwa ga wasu 'yan Najeriya 159, ciki har da tsaffin gwamnoni biyu, Jolly Nyame na jihar Taraba tare da Joshua Dariye na jihar Filato. To sai dai tun wancan lokaci fa wasu jama'a  'yan  Najeriya suka soma nuna shakku  ga ikirarin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na yaki da cin hanci da rashawa.

A jihar Filato dai tun bayan fitowar tsohion gwamna Dariye daga gidan yarin Kuje, wasu jama'ar jihar musaman 'yan asalin karamar hukumar Bokkos maihaifar Dariye, suke ta bukukuwa.

To amma ga Madam Ladi wata 'yar gwagwarmaya sakin Dariye rashin adalci ne wa duk 'yan Najeriya da ke tsare da suka aikata kananan laifuka.

Wasu al'ummar jihar Filato da wakilinmu ya zanta da su na gani cewar sakin tsohon gwamnan bai kamata ba, don kuwa a lokacin gwamnatinsa ne  jihar Filato ta fuskanci tashe-tashen hankula a shekarun  baya,  wasu kuwa cewa suke sakin Joshua Dariye lamari ne daya chanchanta sakamakon halin da ya shiga, yayin da kuma wasu ke daganta lsakin tsaffin gwamnonin  biyu  kan lamari na siyasa tsantsa.