Martanin kasashe da kungiyoyin addinai kan harin Paris | Siyasa | DW | 08.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin kasashe da kungiyoyin addinai kan harin Paris

Duniya na ci-gaba da alhinin harin da wasu mutane uku suka kai kan wata mujallar Faransa da ya kashe mutane 12 tare da raunata wasu masu yawa a ranar Laraba.

Mujallar dai ta taba wallafa zanen batanci wa Annabi Muhammad. Yanzu haka dai shugabannin kasashen duniya da dama sun yi Allah wadai da wannan harin.

A yanzu haka dai yan sandan kasar na ci gaba da binciken mutanen da suka kai hari, da shekarunsu yake 18 da 32 da 34.

Tun a ranar Larabarce dai aka fara gangami a biranen Turai da dama, domin nuna alhini kan harin na kasar Faransa. Dubban jama'a sun taru a biranen London, Berlin, Brussels, da makamantansu domin tunawa da wadanda suka mutu a harin na Charlie Hebdo.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin