1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Israila game da rahoton hukumar IAEA kan Iran

Umaru AliyuNovember 10, 2011

Kasar Israila ta maida martani game da rahoton baya-bayan nan na hukumar makamashi ta duniya, wato IAEA game da manufofin nuclear na kasar Iran tare da kira ga kasashen duniya su hana Iran din ta cimma burin ta.

https://p.dw.com/p/138JD
Shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad a daya daga cikin tashoshin nuclear na kasarHoto: AP

Rahoton na hukumar IAEA ya haifar da martani dabam dabam daga kasashen duniya. Amirka ta kwatanta rahoton a matsayin abin damuwa matuka, Iran kuma tayi watsi da rahoton a matsayin wanda ko kadan bai dace ba, kuma babu wani abu na gaskiya tatare dashi. A daura da haka, kasashen Jamus da Ingila da Faransa sun baiyana buikatar kara tsananta takunkumi kan kasar ta Iran, Rasha kuma tayi adawa da hakan. Israila a daya hannun, tayi kira ne ga kasashe da kungiyoyin duniya su dauki matakai na gaggawa kan Iran tun kafin a makara.

Gwamnatin Israila a wannan karo ma ta kyale fagen martani ne ga yan adawa da kafofin yada labarai, su maida martani game da rahoton na hukumar makamashi ta duniya kan kasar Iran. Saboda haka ne shugabar jam'iyar adawa ta Kadima Zipp Livni tayi magana a gidan rediyon kasar ba ma a madadin jam'iyar ta kadai bane, amma har a madadin mafi yawan yan Israila.

Tzipi Livni Israel Opposition Kadima Partei
Tzipi Livni, shugabar jam'iyar adawa ta Kadima a IsrailaHoto: picture alliance/abaca

Tace yanzu dai komai ya tabbata a fili. Yanzu an gane cewar abin da ake fada ba daga Israila ko wasu majiyoyi ne kadai suka fito ba. Iran tana kokarin samarwa kanta makaman nuclear, saboda haka wajibi ne duniya baki daya ta dakatar da al'amari ne na gwamnatin hadin gwiwa ko na yan adawa ba, ko kuma siyasa ce ta wata gwamnati a Israila ba. Ina kuma so nuna cewar wannan ba matsala ce ta Israila kadai ba, amma al'amari ne da ya shafi duniy abaki daya, wanda kuma duniya tilas ta hana Iran din cimma burin ta.

Marubuta da masharhanta da dama a Israila sun yi nuni da cewar yanzu dai ya rage ne ga kasashe da kungiyoyin duniya su dauki matakin da ya dace kan Iran sakamakon rahoton na IAEA. Sai dai a kasar babu mai sa ran cewar China da Rasha zasu goyi bayan kasashen yamma, domin kara tsananta takunkumi kan kasar ta Iran.

Saboda haka ne Israila din ta baiyana fatan kasashen Turai da Amerika zasu gabatar da wata sabuwar manufa kan wannan matsala. Kasar tana kira garesu, su kara tsananta takunkumi kan Iran, da zai haddasa rushewar tattalin arzikin kasar. Tana son kasashen yamma su ki sayen man fetur daga Iran,su kuma maida ita saniyar ware a hada-hadar kudi na duniya baki daya.

Yan Israila a kan tituna akalla suna baiyana imanin takunkumi kan Iran zai kai ga biyan bukata. Erez Goldmann birnin Kudus ya baiyana abin da mafi yawan yan Israila suke gani, inda yace:

Babbar matsalar mu ita ce kasashen Rasha da China sun kasa fahimtar ainihin barazanar dake fitowa daga kasar Iran. Ko ba ma haka ba, watakila ma har goyon bayada taimakon Iran suke yi. Muddin kuwa basu gane hakan ba, kuma basu hadfa kansu da kasashen yamma da Amerika ba, to kuwa ban ga yadda duk wani sulhu ba, in banda a kaiwa Iran hari.

Wani mazaunin birnin Kudus, Allen Shuchalter shi kuwa yana ganin akwai dangantaka a rikicin na Iran da yakin da Amerika tayi a Iraki.

Yukiya Amano / IAEA / Atomenergiebehörde
Yukiya Amano, shugaban hukumar makamashi ta duniya, IAEAHoto: AP

Yana da matukar hadari kasar da bata cikin kwanciyar hankali kamar Iran a kyale ta mallaki malamai na kare dangi. Amerika ta kaiwa Irak hari ko da shike bata mallakar makaman kare dangi. A ra'ayi na, babu wani dalilin da zai sanya Amerika ta rika jan kafa yanzu kan Iran. Idan har akwai damar cimma burin da ake so ta hanyar takunkumin tattalin arzki to ayi hakan, amma lokacin da ake dashi ba mai tsawo bane. Babu wani dalilin da zai sanya Israila ce zata kasance cikin hadari kan abin da ya kamata ayi, amma ba'a yi ba, wato kawo karshen barazanar da muke fuskanta.

Ministan tsaro Ehud Barak ya baiwa yan kasar sa kwarin gwiwar cewar idan har yaki da Israila ya zama wajibi, to kuwa yan Israila da zasu tagaiyara ba zasu kai dari biyar ba.