Martani kan kamen da jami′an tsaron Najeriya suka yi | Siyasa | DW | 01.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan kamen da jami'an tsaron Najeriya suka yi

Jami'an tsaron Najeriya sun ce sun kama wani da ke da hannu a satar 'yan matan da aka yi a Chibok, abin da ya janyo martani daga al'umma

A Najeriya sanarwar da hedikwatar tsaron ƙasar ta fitar na samun kame wa ni ɗan kasuwa da ta ce shi ne ya kitsa sace ‘yan mata nan sama da 200 'yan makarantar na garin Chibok a jihar Borno. Ya sanya maida martani da ma tambayar ko kame shi ya kwantar da hankalin masu fafutukar ganin an ceto ‘yan mata daga hannun Ƙungiyar Boko Haram.

Sanarwar da jami'an tsaron Najeriyar ta bayar, na kame mutumin da ta bayyana shi a matsayin wanda ke da hannu dumu-dumu a sace 'yan matan na garin Chibok da ma wasu hare-haren da aka kai na zama matakin farko da sojojin suke fatan zai iya taimakan gano bakin zaren matsalar.

Nigeria Boko Haram Entführung 02.06.2014 Maiduguri

Mata na bayyana damuwarsu kann karuwar satar 'yan mata

Mutumin wanda da suka bayyana shi da suna Babuji Ya'ari wanda suka danganta shi da cewar dan leƙen asiri ne ga Ƙungiyar ta Boko Haram da ke faffatawa da gwamnatin Najeriyar yanzu haka ana tsare da shi.

Da ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin