1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ana ci gaba da tsokaci kan furucin Buhari

Uwais Abubakar Idris
February 19, 2019

A Najeriya ana maida martani mai zafi a game da kalaman da shugaba Muhammadu Buhari ya yi a kan masu satar akwatin zabe da ya ce duk wanda ya yi hakan to ya yi ne a hatsarin bakin rayuwarsa,

https://p.dw.com/p/3Depe
Vor Wahlen in Nigeria  Muhamadu Buhari (M), Präsident von Nigeria, und Atiku Abubakar (r)
Hoto: picture-alliance/AP/B. Curtis

Kama daga kungiyoyin kare hakin jama'a da ‘yan siyasa da ma masana a harkar tsaro kusan kowanensu na bayyana  hatsarin da ke tattare da kalaman na shugaban Najeriya da wasu kea fassarar umurni ne ko barazana ta harbi ga duk wanda ya saci akwatin zabe.

A bayyane take a fili cewa shugaban na Najeriya ya fusata da  dage zaben kasar da hukumar zabe mai zaman kanta ta yi da ya kaiga furta wannan kalami. Mallam Auwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar kare hakin jama'a da bunkasa dimukurdiyya ta Cislac ya ce su kam sun damu matuka.

Najeriya dai kasa ce da ta dade da fuskantar zagin jami'an tsaronta da kashe-kashen jama'a ba bisa doka ba, inda wasunsu ke kama da ‘yan bindiga dadi wajen harbi. Abinda ke dalilin aikawa da mutane da dama lahira baya ga wadanda ‘yan ta'ada iri daban-daban ke yi.

Nauyin kalamam da ya sanya samun ra'ayoyin mabanbanta inda kalilan cikin 'yan siyasa ke goyon bayan lamarin, ga Chief Bola Ahmed Tinubu jigo a jamiyyar APC mai mulki da ma majalisar takarar neman shugabanci na jamiyyar ya ce ba'a fahimci abinda shugaban ke nufi ba.

Ana cike da fatan bayyana ra'ayoyin watsi da kalaman zai sanya jami'an tsaron amfani da hankalinsu a dai dai lokacin da wani sashi na sojoji ke baiyyana zasu aiwatar da kalaman bisa umurni na shugaban Najeriyar domin zama lafiya yafi zama dan sarki da ma sarkin kansa.