Martani kan kafa sabuwar gwamnatin Girka | Siyasa | DW | 26.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan kafa sabuwar gwamnatin Girka

Ana ci gaba da mayar da martani bayan jam'iyya mai adawa da tsuke bakin aljihu ta samu galba a zaben kasar Girka

Shugaban jam'iyyar ta Syriza, Alexis Tsipras dan shekaru 40 da haihuwa kana sabon firamnista, ya kafa sabuwar gwamnati tare da jam'iyya mai matsakaicin ra'ayi. Babban aikin da ke gaban sabuwar gwamnatin shi ne warware matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta inda aka kwashe shekaru shida ba tare da samun bunkasa ba.

Lokacin yakin neman zaben Tsipras ya yi alkawarin kawo sauye-sauye more rayuwa da taomakon iyalai da ba za su iya biyan kudaden haya da na wutar lantarki ba, da kara mafi karancin albashi. Jam'iyyar ta Syriza tana burin tsayar da cefanar da kaddarorin gwamnati kamar yadda aka tsara karkashin yarjejeniyar bai wa kasar tallafi.

Jörg Krämer babban jami'an tattalin arziki a bankin kasuwanci na Jamus, ya ce tilas nan gaba kadan sabuwar gwamnati ta fuskanci gaskiya.

Ya kara da cewa zai yi matukar wahala kasar ta iya biyan kudaden da ake binta bashi kimanin euro bilyan hudu da rabi. Masana na ganin yuwuwar kasar ta fada matsaloli idan ta daina karbar bashi, zuwa lokacin bazara, saboda daga lokacin za ta sake neman kimanin euro bilyan uku da rabi.

Jens Weidmann shugaban babban bakin Jamus, ya yi gargadin cewa sabuwar gwamnatin Girka ba za ta iya cika alkawarin da ta dauka ba lokacin yakin neman zabe.

Sabuwar gwamnatin kasar ta Girka karkashin jam'iyyar Syriza tana kara jan layi tsakani da sauran kasashen Turai masu amfani da kudin bai daya na Euro. Sai dai Jörg Krämer babban jami'an tattalin arziki a bankin kasuwanci na Jamus, yana ganin sabon firamnistan kasar ta Girka Alexis Tsipras da jam'yyarsa ta Syriza sun wuce gona da iri kan neman sake tsara shirin ceto tattalin arzikin kasar, kuma babu wata nasara da za su samu.

Masana na ganin cewa masu ba da bashi za su amince da wata matsaya da sabuwar gwamnatin, domin kowani bangare ya yi sassauci. Fitar kasardaga cikin kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro zai iya jefa kasuwannin hannun jari cikin gadari.

Sauti da bidiyo akan labarin