Martani kan ci gaba da binciken gwamman Kano | Siyasa | DW | 07.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani kan ci gaba da binciken gwamman Kano

Ana mayar da martani bisa matakin majalisar dokokin jihar Kano da ke Najeriya na ci gaba da binciken zargin cin hanci ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje duk da umurnin kotu.

Masana da sauran Jama'a na ci gaba da martanin kan matakin da majalissar dokokin jahar Kano da ke Najeriya ta dauka na ci gaba da bincikien Gwamna Abdullahi Umar Ganduje  na jihar bisa zargin sa da karbar na goro a hannun 'yan kwangila, wanda jaridar Daily Najeria ta wallafa hoton bidiyon da ke nuna gwaman na karbar na goro a hannun 'yan kwangila, duk kuwa da cewar wata babbar kotu a jihar ta ba da umarni ga kwamitin da ke gudanar da binken kan dakatar da ci gaba da binciken.

Kwammitin nan majalisar dokokin jihar ta Kano ya ce za su ci gaba da bincken da suka fara game da neman sanin gaskiyar, saboda umurnin da kotu ta bayar bai hana su gidanar da aiki ba. Sai dai lamarin ya janyo martani inda wasu lauyoyi ke ganin ya dace majalisar dokoki ta bi umurnin kotu, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci, kamar yadda kotun ta bukata.

Sauti da bidiyo akan labarin