Martani a kan sauke shugaban SURE-P | Siyasa | DW | 11.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martani a kan sauke shugaban SURE-P

A Najeriya cire shugaban shirin tattarawa da aiwatar da kudaden ribar rarar man fetur domin tallafawa talakawa da shugaban Najeriya ya yi, ya haifar da mayar da martani.

Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan

Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan

Bayanai na nuni da cewa tsige shugaban shirin na SURE-P Janar Martin Luther Agwai ya biyo bayan kalaman da ya furta na cewa ana bukatar canji. Al'ummar Tarayyar ta Najeriya dai na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan illar da sauke Janar Agwai din ka iya yi ga yanayin shugabanci a kasar. Shi dai shugaban shirin na SURE-P Janar Agwai ya furta kalaman ne a wajen walimar cika shekaru 78 da haihuwa ga tsohon shugaban Tarayyar ta Najeriyar Olusegun Obasanjo, wanda aka dade da ganinsu a rana tsakaninsa da fadar shugaban Najeriyar. Wannan ya sanya danganta batun sauke shin da dalilai na siyasa ba wai kawai sauyin shugaba ga shirin na SURE-P ba. Janar Luther Agwai dai ya fito karara tare da bayyana cewa babu fa zabi ga canji kuma akwai bukatar shugabanni su karbi canji a duk lokacin da ya zo musu.

Tsohon shugaban Tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban Tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo

Kin gaskiya da amfani da siyasa

Malam Hasan Dawaki mai sharhi ne a kan al'ammuran yau da kullumn ya bayyana illar da ke tattare da cusa siyasa a batu na gudanar da harkokin mulki a Najeriya, inda ya ce gwamnati na ganin da ka fadi gaskiya ka zama dan adawa, ya kuma ce hakan zai kara durkusar da kaifin mulki da ma jam'iyyar da ke mulkin. A bayyane ta ke a fili dai gwamnatin shugaba Jonathan da ta dage wajen kokarin ganin ta zarce a kan mulki a zaben da ake shirin gudanarwa, ba ta boye adawarta ga wannan kalma ta canji.

Yarfe ne irin na siyasa

Rashin aikin yi ga matasan Najeriya na taimakawa wajen tayar da zaune tsaye

Rashin aikin yi ga matasan Najeriya na taimakawa wajen tayar da zaune tsaye

A kwanakin baya dai uwargidan shugaban Najeriyar Patient Jonathan ta bayyana cewa duk wanda ya furtawa mutanen jiharta kalmar canjin to su yi mashi ruwan duwatsu abinda ake ta cece kuce a kansa. Bangaren gwamnati da ma jam'iyyar PDP dai na ganin yarfe ne kawai na siyasa danganata kalaman da Janar Agwai din ya yi da batun tsige shi. Barrister Abdullahi Jallo shine mataimakin sakakataren yada labarai na jamiyyar PDP da ke mulki, ya kuma ce shugaban kasa ne ya nada shi kuma dokar da ta ba mutum izinin nadawa to ta bashi na cirewa.