1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maroko ce kasa ta hudu da ta dawo da hulda da Isra'ila 

Yaya Azare Mahamud AMA
December 11, 2020

Kasar Maroko ta bi sahun kasashen Larabawan da suka kulla alaka da Isra'ila, bayan Amirka ta aminta da ta mallaki yankin yammacin Sahara da ake rikici tsakaninta da 'yan Polisario.

https://p.dw.com/p/3maXE
Bildcombo I Benjamin Netanyahu ,Donald Trump, König Mohammed VI
Benjamin Netanyahu da Donald Trump da Sarki Mohammed VI na Maroko

Shugaban Amirka Donald Trump ya zama uwa da makarbiyar kulla huldar kasashen Larabawa da Isra'ila, inda ya sanar da cewa kasar Maroko ta mayar da dangantakar diflomasiyyarta da Isra'ila, a yayin da ita kuwa Amirka ta nuna amincewa da halaccin Maroko na mallakar yankin yammacin Sahara da 'yan Polisario ke fafutukar kafa kasarsu mai cin gashin kanta.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya siffanta wannan jingar da "haske bisa haske" inda ya ce sannu a hankali ke haskaka tarun duhun da ya jima yana mamaye yankin Gabas Ta Tsakiya yana mai cewa "Hasken zaman lafiya bai taba bayyana karara a Gabas ta Tsakiya kamar wannan lokacin ba, ina gode wa Shugaba Trump kan wannan halaccin da ya nunawa Isra'ila, godiya ta musamman sarkin Maroko kan wannan matakin bajintar da ya dauka."

Karin Bayani: Alakar Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa

Marokko - Libyen Diplomatie | Nasser Bourita
Ministan harkokin wajen MarokoHoto: Getty Images/AFP/F. Senna

Ministan harkokin wajen Maroko ya bayyana dawo da huldar a matsayin wani abin da ba na mamaki ba, yana cewa "Muhimmin batun shi ne yadda Amirka ta amince da halaccin mallakawa Maroko yammacin Sahara." 'Yan asalin Maroko miliya daya ne ke rayuwa yanzu haka a kasar Isra'ila, Marokon ta ce za ta yi amfani da wannan dama ta sake dawo da huldar kasar da Isra'ila wajen jaddada wannan alakar don cin amfanin kasashen biyu. Hukumar Falasdinawa ta siffanta kulla yarjejeniyar da rashin lisafin Maroko da cin amanar al'ummar Falalsdinawa, tare da bayyana yarjejeniyar da ake ci gaba da kullawa tsakanin Isra'ila da kasashen Larabawa a matsayin wata gadar zare, wacce da wuya gwamnatin Joe Biden ta amince da ita.