1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manyan zabuka a kasashen Afirka da dama

Mohammad Nasiru AwalOctober 29, 2015

A kasashen Cote d'Ivoire da Tanzaniya an gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki yayin da al'ummar Kwango-Brazzavile suka kada kuri'ar raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/1GwXB
Tansania Wahlen
Hoto: Reuters/S. Said

Zabubbukan dai sun gudana cikin wani yanayi na kwanciyar hankalin da lumana musamman a kasar Cote d'Ivoire, yayin da a Tanzaniya, musamman a tsibirin Zanzibar aka fuskanci kura-kurai da zargin aringizon kuri'u. A Jamhuriyar Kwango an fuskancin karancin fitowar masu zabe.