Soke zaben tsibirin Zanzibar ya jefa sakamakon zaben Tanzaniya cikin shakku | Labarai | DW | 28.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Soke zaben tsibirin Zanzibar ya jefa sakamakon zaben Tanzaniya cikin shakku

Ana zaman zullumi da rashin tabbas kan bayyana sakamakon zaben Tanzaniya, bayan an soke zaben a tsibirin Zanzibar mai 'yancin cin gashin kai.

An shiga cikin rudu a zabukan da aka gudanar a Tanzaniya biyo bayan soke zaben tsibirin Zanzibar da ke cikin hadaddiyar Jamhuriyar Tanzaniya amma ke da kwarkwaryar 'yancin cin gashin kai. Soke zaben tsibirin ya janyo zaman zullumi, sannan ana saka ayar tambaya game da yiwuwar bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a ranar Alhamis. Jam'iyyun adawa sun yi zargin tabka magudi a zabukan na ranar Lahadi, inda jam'iyyar da ke jan ragamar mulki ta fuskanci kalubale mafi girma cikin shekaru gommai da ta rike madafun iko. Sai dai tawagogin sa ido a zabe sun yaba da yadda zaben ya gudana, in ban da wasu kurakurai da aka fuskanta. Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da ya jagoranci tawagar kungiyar Commonwealth da ta sa ido a zaben ya yi karin haske:

Ya ce: "Ba mu dai yi karin bayani ba domin wannan shi ne rahotonmu na farko, har yanzu muna jira ga misali daga Zanzibar domin a can ake cikin zullumi. Amma mun yaba da zagayen farko na zaben wato shirye-shiryen zaben."