Tanzaniya tana cikin kasashen yankin gabashin Afirka wadda ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya a 1961 lokacin ana ce mata Tanganyika.
Kasar ta koma Tanzaniya a shekarar 1964 bayan hadewa da tsibirin Zanzibar, kuma tana cikin kasashen Afirka da suka kauce wa juyin mulki na sojoji. Ana amfani da Ingilishi da kuma Swahili a matsayin harshen kasa.