1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

100709 Obama Afrika Politik

July 10, 2009

A juma'ar nan ce shugaban Amurka Barak Obama yake kai ziyararsa ta farko ga nahiyar Afurka, inda takanas zai ya da zango a ƙasar Ghana.

https://p.dw.com/p/IlJH
Kwalin hoton shugaba Atta Mills na Ghana da shugaban Amirka Barak ObamaHoto: AP

Dukkan jami'an siyasa da al'umar Afurka sun saka dogon buri akan sabon shugaban na Afurka. To ko shin a haƙiƙa za'a samu canjin manufofin Amurka dangane da nahiyar Afurka a ƙarƙashin shugaba Barak Obama.

Ghana dai a halin da ake ciki yanzu tana a matsayin abin koyi ne a fannoni na siyasa da ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afurka. Kuma wannan shi ne ainihin dalilin da ya sanya fadar mulkin Amurka ta White House ta zaɓi ƙasar don zama ta farko da shugaba Obama zai kai wa ziyara a nahiyar Afurka. Akwai kuma wasu dalilan dabam, kamar yadda Machaia Munene, masanin kimiyyar siyasa daga ƙasar Kenya ya nunar:

Ya ce:"Ghana wata alama ce mai muhimmanci a tarihi. Ita ce ƙasa ta farko da ta samu 'yancin kanta tsakanin ƙasashen Afurka. A sakamakon haka ƙasar ta zama shaidar 'yancin kai a ƙarƙashin tsofon shugabanta Kwame Nkrumah, ba ma ga nahiyar Afurka kaɗai ba, hatta ga ƙungiyoyin fafutukar neman haƙƙin farar fula a Amurka.Fatana shi ne Obama zai yi amfani da wannan ziyarar domin gabatar da cikakken saƙo a game da manufofin Amurka dangane da Afurka. Saboda kawo yanzu hakan bata samu ba."

Ita dai Ghana ta samu nasara a inda da yawa daga cikin ƙasashen Afurka suka gaza, musamman ma a game da ire-iren abubuwan da Amurka ke so ta ba wa goyan baya a nahiyar, wato ci gaban tattalin arziki da siyasa da amfani da albarkatun ƙasa daidai yadda ya kamata da ɗaukar nagartattun matakai wajen tinkarar matsalar talauci da ilimi. A baya ga haka akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin Ghana da Amurka, lamarin dake da muhimmanci ga ziyarar shugaba Obama kamar yadda aka ji daga bakin Nicolas van de Walle masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Coenell Ithaka dake birnin New York:

Ya ce:"Zaɓar ƙasar Ghana da aka yi na mai yin nuni ne da muhimmancin mulki na gari a ƙarƙashin tsarin demoƙraɗiyya tsantsa da kuma ci gaban tattalin arzikin ƙasa. Wannan shi ne babban dalili. Ghana ƙasa ce nagartaccen tsarin mulkin demoƙraɗiya a Afurka."

Kazalika zaɓar wata ƙasa ta ƙawance kamar Ghana abu ne dake yin nuni da cewar gwamnatin Obama zata bi saun ta Bush a manufofinta dangane da nahiyar Afurka. Domin kuwa gwamnatin Bush sai da ta ɗaga martabar Ghana a manufofinta saboda muhimmancin da nahiyar ke da shi a fannoni na tattalin arziki da al'amuran tsaro da kuma kandagarkin kasancewar ƙasashen Afurka dandalin renon 'yan ta'adda. Sai dai kuma abin da ya kamata a lura da shi shi ne kasancewar hatta a ƙarƙashin shugaba Obama, wanda mahaifinsa ɗan usulin Kenya ne, Amurka ba zata bai wa Afurka fifiko a manufofinta na ƙetare ba duk da dogon burin da da yawa daga al'umar nahiyar suka saka a zukatansu a game da shugaban, wanda shi ne na baƙar fata na farko da ya shugabanci ƙasar ta Amurka.

Mawallafa: Ute Schaeffer/Ahmadu Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal