1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya nada babban hafsan sojin kasa

Abdul-raheem Hassan
May 27, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a mastayin sabon shugaban hafsohin tsaron kasa, bayan mutuwar Janar Ibrahim Attahiru.

https://p.dw.com/p/3u44H
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Sabon shugaban sojojin kasa Manjo Janar Faruk Yahaya shi ne ke jagorantar yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya gabannin nada sgi a sabon mukamin, ya kuma taba rike mukamin kwamandan rundunar sojin kasa ta matakin farko.

A ranar 21 ga watan Mayu na 2021 ne tsohon Shugaban sojojin kasa Lieutenant Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya rasu da wasu dakarun kasa a hatsarin jirgin sama.