1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maniyatta sun hallara birnin Makka

July 17, 2021

A wannan Asabar din ce, cikin tsauraran matakan kariya daga kamuwa da cutar Corona maniyyata aikin hajjin bana suka fara sauka birnin Makka domin gudanar da aikin hajjin.

https://p.dw.com/p/3wd73
Weltspiegel 10.05.2021 | Corona | Saudi-Arabien Mekka | Gebet mit Abstand
Hoto: Saudi Press Agency VIA REUTERS

Manyan motocin safa-safa ne su ka kawo maniyatan babban masalacin birnin mai tsarki inda suka fara da Dawafi, sai dai mutane dubu shida ne aka amince su yi dawafin a lokaci guda, sai bayan sun kammala sannan wasu su shiga.

Wannan dai shi ne karo na biyu ana gudanar da aikin hajjin tun bayan barkewar annobar ta Corona ko COVID-19. A bana mutane dubu sittin ne kacal wadanda aka yi wa rigakafin cutar mahukuntan Saudiyya suka amince su gudanar da aikin a maimakon sama da miliyan biyu da ke gudanar da aikin a baya.