Lafiya
Zazzabin cizon sauro a Najeriya
October 9, 2018Talla
Lamarin da ya zamo jiki ga mutane, inda da zazar anji jiki babu dadi sai a ta hadiyar maganin zazzabin cizon sauraro ba tare da ziyartar Likita ba. Wannan cuta kusan ta zamewa mutane jiki a Najeriya, inda za a tarar da a kalla mutum biyu cikin ko wane gida suna fama da cutar, da zarar kuwa aka ce dare ya yi, sai a ta tururuwar zuwa sayen maganin sauro na hayaki iri-iri, domin turara ko ina, dan korarsu, wasu kuma su bude gidan sauronsu da ake kira ''Mosquito Net'' a turance. Shin ita kuwa, wace irin cuta ce wannan da ta addabi mutane? Ku saurari shirin domin jin karin bayani.