1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cisse ya samu 'yanci daga 'yan ta'adda

October 9, 2020

Hukumomi a Mali, sun sanar da sakin mutanen nan hudu da 'yan ta'addan arewacin kasar suka yi garkuwa da su na tsawon shekaru, ciki har da madugun 'yan adawa Soumaïla Cissé.

https://p.dw.com/p/3jh4e
Soumaïla Cissé
Soumaïla Cissé da shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali Bah N'Daw Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst des Premierministers von Mali

'Yan ta'addan arewacin Mali sun sako madugun adawar kasar Soumaïla Cissé da wata ma'aikaciyar agaji daga Faransa. Mutanen da suka yi garkuwa da su, ciki har da madugun 'yan adawar kasar Soumaïla Cissé. Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Bah N'Daw ya tarbi mutanen ranar Alhamis a fadarsa da ke birnin Bamako, bayan 'yanto su daga arewacin kasar. Wani jirgin agaji dauke da mutanen da aka yi garkuwa da su ya sauka a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na birnin Bamako dauke da mutanen da aka yi garkuwar da su na tsawon lokaci ciki har da madugun 'yan adawar kasar Soumaïla Cissé.

Karin Bayani: Shirin kafa gwamnatin rikon kwarya

Jim kadan bayan ganawa da shugaban kasar Malin na rikon kwarya, madugun 'yan adawar Soumaïla Cissé ya bayyana ranar a matsayin ta farin ciki: "Ina matukar farinciki a yau, bayan na kwashe tsawon watanni shida a hannun masu garkuwa da ni, a cikin wani yanayi na mawuyacin hali da suka hada da kadaici a yankin na sahara. Sai dai ina tabbatar da cewar ba wani abin da na fuskanta daga hannun masu garkuwa da ni kamar cin zarafi ko wata muzgunawa ta jiki har ma da ta fatar baki."

Mali Präsident Bah N'Daw mit Sophie Petronin
Sophie Petronin ma'aikaciyar agaji 'yar Faransa da 'yan ta'addan Mali suka sakoHoto: Presse- und Kommunikationsdienst des Premierministers von Mali

Sophie Pétronin ma'aikaciyar jin ka nan Bafaranshiya tilo da ta rage a hannun 'yan ta'adda a yankin Sahel, tun a shekarar 2016, na daga cikin wadanda 'yan ta'addan suka saka. Haka kuma akwai 'yan kasar Italiya guda biyu da suma suka jima a hannun baraden kungiyar nan mai da'awar jihadi ta GSIM, wacce ta ke da alaka da al-Qa'ida a yankin arewacin Afirka.

Karin Bayani:  Rashin tabbas kan zaman lafiya a Mali da Sudan ta Kudu

Farin ciki maras mislatuwa ya bayyana a tawagar iyalin Sophie ciki har da danta da ya shafe tsawon shekaru yana gwagwarmayar neman 'yancinta. Da take jawabi ga manema labarai, Sophie Pétronin ta bayyana farin cikinta tana mai cewa: "Ina godiya ga hukumomin Mali da gwamnatin Faransa kan kokarin da suka yi wajen ganin na samu 'yancina daga hannun masu garkuwa da ni. Na shafe tsawon shekaru ina aikin kula da yara a yankin arewacin Mali, kuma abin farinciki ne jin cewa abokan aikina sun ci gaba da wannan jan aikin a lokacin da nake tsare."

Rahotanni daga Malin na cewar, an yi musayan mutanen da aka yi garkuwar da su ne da wasu fursunonin yaki na kungiyar 'yan ta'adda kimanin 200 da gwamnatin Mali ke rike da su a gidajen yari.