1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali

September 22, 2020

Biyo bayan kai ruwa rana tsakanin masu juyin mulki a Mali da kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afrika ta Yamma, wato ECOWAS ko CEDEAO, jagoran juyin mulkin Assimi Goita ya sanar da nada shugaban rikon kwarya.

https://p.dw.com/p/3ir3h
Ausschnitt | Mali Bamako | Jean-Ayves Le Drian und Bah N'Daw
Sabon shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali Ba N'DaouHoto: Habibou Kouyate/AFP/Getty Images

Jagoran juyin mulkin na Mali dai Assimi Goita ya bayar da sanarwar nada Ba N'Daou a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya a Mali. An dai bayyana Ba N'Daou a matsayin sabon shugaban gwamnatin rikon kwaryar ta Mali, a ranar Litinin 21 ga wannan wata na Satumba da muke ciki, kuma zai sha rantsuwar kama aiki a ranar Jumma'a 25 ga watan na Satumbar da muke ciki. N'Daou ya kasance tsohon ministan tsaron kasar da ya shiga aikin soja tun yana da kananan shekaru a tsakiyar shekarar 1970, inda ya samu horo daga tsohuwar Tarayyar Soviet.

Karin Bayani: ECOWAS na son maido da zaman lafiya a mali

Ya kuma taba samun horo a kwalejin yaki ta Elite Ecole de Guerre da ke kasar Faransa. Tsohon matukin jirgin sama mai saukar ungulu, ya kuma taba zama shugaban sojojin kasar ta Mali. Daga shekarun 1968 zuwa1991, N'Daou ya kasance babban dogarin tsohon shugaban kasar Malin Moussa Traore. Sabon jagoran ya bar aiki a matsayin kanal a rundunar sojojin kasar.

Karin Bayani: Mali: Matakan kafa gwamnatin rikon kwarya

Kanal Ba N'Daou mai ritaya kuma tsohon minista a ma'aikatar tsaro karkashin hambararren shugaban Malin Ibrahim Boubakar Keita wanda shi ne ma mukaminsa na karshe tun a shekara ta 2014, ya yi ritaya gabanin sanarwar nadin da aka yi masa a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar kasar da aka ratayawa alhakin sake mika mulki ga wata sabuwar zababbar gwamnantin farar hula da al'ummar kasar za su zaba nan da watanni goma sha takwas.