Ko mecece makomar kasar Mali?
May 27, 2021Shugaban Mali na rikon kwarya Bah Ndaw da firaministansa Moctar Ouane sun sanar da ajiye aikin nasu ne, kwanaki biyu bayan da soji suka yi musu juyin mulki kana suka tsaresu. Majalisar Dinkin Duniya da ma ECOWAS da sauran kasashen duniya, sun bukaci a sakesu kana a mayar da kasar kan turba ta mulkin dimukuradiyya.
Sai dai duk da haka sabanin yadda mutane suka fito yin zanga-zangar murna da kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan bara, a wannan karo jama'a da dama sun fito nuna kyama ga matakin kwace mulkin da sojojin suka sake yi.
Ana iya cewa dai, a yanzu babu tabbas kan halin da Malin za ta tsinci kanta a ciki, ganin cewa an yi juyin mulkine ne kasa da shekara guda da kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita tare da kafa gwanatin wucin gadi. An dai amince gwamnatin za ta mika mulki ga farar hula daga bisani. Sai dai kuma da wannan sabon juyin mulki, abin tambayar shi ne: Ina Mali ta dosa?