1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan Malawi sun ja hankali kan muhalli

Abdul-raheem Hassan
November 9, 2021

Matasan Malawi sun yi kashedin cewa muddin shugabanni ba su sanya matasa cikin shirye-shiryen sauyin yanayi ba, yunkurin rage sauyin yanayi ba zai yi tasiri ba.  

https://p.dw.com/p/42n8Q
Demonstration in Durban während der Weltklimakonferenz
Hoto: dapd

Matasan Malawi sun yi zanga-zanga a Lilongwe babban birnin kasar. Suna neman yin magana game da muhimmancin dakatar da barazanar sauyin yanayi. Yawancin waɗannan matasan suna jin cewa yawancin matasa ba su da sha'awar shirin rage sauyin yanayi da shirye-shiryen dai-daito.

Nsaiwale Mwale mai shekaru 31, ya kafa wani shiri inda ya kware wajen sarrafa shara amma har yanzu yana da wuya ya kutsa cikin kasuwa.

BG FFF weltweit Protestaktion in Kapstadt
Hoto: Reuters/M. Hutchings

"Tsofaffi ba za su rayu su ga abin da sauyin yanayi ya yi ba, amma wadannan matasa su ne za su zauna da shi, kuma dole ne su sha wahala, don haka lokaci ya yi da ya kamata mu matasa mu tashi tsaye mu dauki mataki a yanzu."

Shugabannin kasashen duniya na ganawa kan sauyin yanayi a birnin Glasgow domin tattauna hanyoyin rage hayakin CO2 da kuma kare dazuzzuka na duniya.

Sai dai Lisa Banda ta zargi shugabannin da kasa cika alkawuran da suka dauka. Ta ba da misali da gudunmawar dala biliyan 100 na shekara-shekara da aka fara a shekara ta 2020 da kasashe masu arziki ke bayarwa wadanda ba a bai wa kasashe masu tasowa ba musamman a Afirka. Yarjejeniyar da aka kwashe shekaru 10 ana yi tana nufin taimakawa kasashe matalauta su canza zuwa makamashi mai tsafta da kuma daidaita sauyin yanayi.

Archivbild Demonstration in Durban UN Klimakonferenz
Hoto: Getty Images/AFP/S. de Sakutin

"Muna neman kasashe su mutunta alkawarin dala biliyan 100 da aka dau nauyin kula da sauyin yanayi. Wato, muna son ba wai kawai a maida hankali kan ragewa ba, amma muna son ya zama rabon 50/50, duka biyun ragewa da daidaitawa.".

Jama'a da dama sun yaba wa matashiya mai fafutukar sauyin yanayi ta kasar Sweden Greta Thunberg, bisa yadda ta zaburar da matasa don daukar mataki kan ajandar sauyin yanayi. Wannan matashi dan kasar Malawi, na ganin lokacin yayi da sauran matasa za su taka rawar gani sosai.

"Matasa na iya daidaitawa cikin sauƙi kuma suna iya rayuwa cikin sauƙin rayuwa marar amfani. Don haka ina ganin dole ne a saka matasa a yawancin shirye-shiryen, kada a bar matasa, mu kasance a kan gaba."

Matasan da suka yi zanga-zangar lumanar a Malawi, sun hade da jerin masu fafutukar kare muhalli, inda suke daga murya ga shugabannin kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa na dai-daita dumamar yanayi.