1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a dawo da kayan tarihin Benin

Uwais Abubakar Idris AH
May 30, 2023

Cibiyar raya al'adun kasar Jamus ta Goethe ta gudanar da tattaunawa kana muhawarar da ta taso game da makomar kayan tarihi na masarautar Benin da ta fara dawo wa Najeriya da su.

https://p.dw.com/p/4Ryb0
Benin Bronzen
Hoto: Florian Gaertner/photothek/IMAGO

Kwararru a fanin kula da sassake-sassake na kayan tarihi ne suka hallara a kokari na kalailaice makomar kayan tarihin masarautar Benin din da Jamus ta fara dawowa Najeriya da su. Kama daga batun darajarsu da amfani a matsayin kayan tarihi da sassake-sassake da masarautar Benin a Najeriya, da yadda za su samar da kafa ta samun kudin shiga. Ra'ayoyin sun sha bamban a kan tsoron da ake yi kan makomarsu musamman a hannun basaraken Benin kamar yadda gwamnatin Najeriya ta ayyana maimakon hukumar kula da kayan tarihi. Ko yaya kasar Jamus da ta amince bisa yarjejeniya za ta maido da kayayyaki ta ji da wannan sauyi daga gwamnati da a yanzu aka bai wa Oba na Benin ikon malaka da kulawa da kayan tarihi? Mr Martin Huth shine mataimakin jakadan kasar Jamus a Najeriya.

Sake dawo daga kayan tarihin daga Jamus zuwa Najeriya abin farin ciki ga 'yan Najeriya

Hamburg Ausstellung „Benin. Geraubte Geschichte“
Hoto: Daniel Reinhardt/dpa/picture alliance

Ya ce: ''Muna farin cikin ganin an maido da kayayyakin na tarihi na Benin zuwa Najeriya, mu a nan ba mu da wata damuwa a kan ina za'a kai kayan wannan batu ne na Najeriya. Babu shakka za mu yi farin cikin ganin an baje kolin kayan tarihi a ajiye su inda kowane mutum zai iya zuwa ya gani, mun san za'a sulhunta dukkanin batutuwa a tsakanin ‘yan Najeriya, amma ina cewa wannan shawara ce ta ‘yan Najeriya''. A yayinda ake wannan muhawara a kan makomar kayayyakin tarihi na masarautar Benin din da gwamnatin Jamus ta fara maidowa, shin wannan mataki ne na diplomaisyya ko taimaka wa Najeriyar ce? Muhammad Suleiman shugaban kungiyar masu fasahar zane-zane da saasaka kaya tarihi ta Najeriya ya ce abu ne mai kyau. Abin da ya bayyana a karshe shi ne duk da nuna damuwar da ake yi a kan makomar kayayyakin tarihin, akwai tanajin na adana bayanan kayan tarihin Benin inda babu yadda za'a sake daukansu a sayar da su a duniya