Majalissar Amirka na shirin sauraren Hillary Clinton | Labarai | DW | 25.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalissar Amirka na shirin sauraren Hillary Clinton

Komitin bincike na majalissar dokokin akar Amirka zai saurari bahasi daga Hillary Clinton kan batun mutuwar jakadan Amirka a Benghazi a 2012

A kasar Amirka Hillary Clinton ce ke shirin bayyana a gaban wani komitin bincike na Majalissar Dokokin kasar domin bayar da bahasi a kan harin ta'addancin da wasu suka kaiwa ofishin jakadancin kasar ta Amirka a birnin Benghazi da ya yi sanadiyyar mutuwar jakadan kasar ta Amirka a kasar ta Libiya dama wasu makarrabansa ukku a ranar 11 ga watan Satimba na 2012.

Wani kakakin Hillary Clinton wacce ke shirin tsayawa takara a zaben shugaban kasa mai zuwa a kasar ta Amirka ne ya tabbatar da wannan labari a Assabar din nan inda ya ce za ta bayyana a gaban komitin majalissar ne ranar 22 ga watan Octoba mai zuwa.