1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar wakilan Amurka na duba dokar Bush akan wadanda ake zargi da taaddanci

September 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bui7

Yan jamiyar republican a majalisar wakilai ta Amurka a yau sun fara matsa kaimi domin ganin wucewar kudirin doka ta Bush dake neman tursasawa wadanda ake zargi da laifin taaddanci.

A nasu bangare yan jamiyar demokrats suna ci gaba da sukar wannan doka,suna masu cewa hakan zai bashi damar muzantawa wadanda ake zargi tare da kara hanyoyin azabtarda wadanda akeyiwa tambayoyi game da laifukan taaddanci.

Yar majalisa Ellen Taucher tace amincewa da wannan doka zai bada dama ga wasu kasashe su azabtar da sojojin Amurka da suka tsare.

Duk kuwa da adawa da akeyi , ana sa ran majalisar wakilan zata amince da dokar a karshen zamanta na yau.