Majalisar dinkin duniya ta ja kunnen Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 29.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Majalisar dinkin duniya ta ja kunnen Sudan ta Kudu

Sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya bukaci Sudan ta kudu da kada ta kunyata al'ummomin kasashen duniya bayan alwashin shugaban kasar kan aiwatar da yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a kasar.

A yayin da yake jawabi a zauran taron Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-moon jim kadan bayan da Shugaba Salva Kirr ya kammala jawabin sa, yace a shirye muke mu taimaka muku, bama zaton kuma zaku kunya ta mu.

Kasashen duniya dai na fatan jadawalin shirin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka tsara a watan Augustan daya gabata zai kai ga samar da tabbatuwar zaman lafiya a Sudan ta Kudu da yakin basasa ya yi wa fafata tun a shekara ta 2013.