1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram sun lalata hanyoyin wutar lantarki

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
February 2, 2021

Ana fama da matsalar wutar lantarki a birnin Maiduguri na yankin Arewa maso gabashin Najeriya kwanaki bayan mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari.

https://p.dw.com/p/3okj5
Nigeria University Maiduguri
Hoto: Alamin Muhammed/DW

Ana zargin kungiyar ISWAP mai ikrarin jihadi a yammacin Afirka da alhakin kai hari, wanda shi ne karo na uku da mayakan Boko Haram ke kaddamar da harin a jihar ta Borno ta Najeriya, jihar da yaki da masu da'awar jihadi ya daidaita.

Birnin Maiduguri da ke zama fadar gwamnatin jihar Borno inda mayakan na Boko Haram suka fi kai hare-hare, ya tsinci kanshi cikin mawuyacin hali daga mayakan tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da sauke hafsoshin tsaron kasar tare da maye gurbinsu da sabbi.