Mahukuntan yankin Hong Kong sun fitar da jadawalin zabe | Labarai | DW | 22.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mahukuntan yankin Hong Kong sun fitar da jadawalin zabe

Tsarin zaben dai bai nuna wata mutuntawa ba ga bukatun masu fafutikar demokradiya a yankin da suka sha fama da zanga-zanga a bara.

Yankin na Hong Kong da ke wani bangaren China, a yau Laraba suka bayyana jadawalin da zai kai ga zaben jagorori daga yankin, tsarin kuma da ke nuna cewa babu zancen daga kafa ga masu fafutikar demokradiya. Batun kuma da ya sanya dan majalisa daga bangaren adawa ya fice daga wajen taron bayyana wannan shiri.

A cewar babbar sakatariyar da ke wakilitar gwamnatin kasar ta China a yankin na Hong Kong, Carrie Lam, zabin kujerar koli daga yankin da ke zama karo na farko a tarihi karkashin demokradiya, za a yi shi ne bisa kulawa da bin sharuda na majalisar al'ummar kasar ta China NPC.

A karkashin tsarin dai 'yan takakara da za su nemi kujeru manya daga yankin na Hong Kong, dole su kasance amintattu ne da kwamitin majalisar ya amince da su , lamarin da ya jawo zazzafar zanga-zangar masu rajin demokradiya a yankin, a karshen bara.