1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta tarbi mahajjatan bana

Abdul-raheem Hassan
June 4, 2022

A karon farko bayan shekaru biyu, hukumomin Sauduyya sun tarbi rukunin farko na maniyyata aikin hajji daga kasar waje. Tun a shekarar 2019 maniyyata daga kasashen ketere ba su zuwa aikin hajji saboda annobar corona.

https://p.dw.com/p/4CI62
Haj und Eid Al Adha 2021
Hoto: Saudi Ministry of Media/REUTERS

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ce kasar Indonesiya ce kasa ta farko da ta sauka a birnin Madina, kuma za ta yi tattaki zuwa birnin Makkah da ke kudancin kasar domin shirin gudanar da aikin hajjin 2022.

An kiyasata mutane miliyan 2.5 ne suka sauke farali a shekarar 2019 gabannin bullar cutar corona a duniya, amma 2020 hukumomin Saudiyya sun ba wa maniyyata 1,000 kacal izinin aikin hajji.

Duk da janye dokar haramta zuwa aikin hajjin saboda corona, hukumomin sun ce duk masu zuwa daga wajen Saudiyya wajibi su nuna shedar ba su dauke da cutar da kuma gwajin yin tafiya wanda bai wuce sao'i 72 ba.