1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron: Zanga zanga ba ita ce mafita ba.

Abdullahi Tanko Bala
November 27, 2018

Duk da cewa ya amince da damuwar da jama'a suka nuna game da karin haraji kan man fetur, shugaban Faransa Emmanuel Macron yace ba zai sauya manufarsa game da kare muhalli ba.

https://p.dw.com/p/390CJ
Frankreich Emmanuel Macron in Albert
Hoto: Reuters/P. Wojazer

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kokarin yayyafa wa wutar rikicin zanga zangar adawa da gwamnatinsa ruwa kan batun karin haraji kan man fetur yana mai cewa ya ji koken masu zanga zanga amma ba zai sauya matsayinsa ba.

Shugaban mai shekaru 40 da haihuwa yace ya amince cewa mutane da dama na ganin karin harajin yayi tsauri abin da ya haddasa zanga zanga da aka shafe kwanaki 1o ana yi a kwanakin baya

A jawabin da ya yi kan manufofin gwamnatinsa kan makamashi Macron ya ci alwashin ci gaba da aiwatar da manufofi wadanda za su dace inganta yanayin muhalli. 

Yace akwai bukatar sauya yadda ake tafiyar da lamura. 

Ya kuma yi alkawarin tattaunawa da masu zanga zangar da kuma dukkan masu ruwa da tsaki domin samun masalaha cikin watanni uku masu zuwa.