Macron zai kawo sauyi a Tarayyar Turai | Labarai | DW | 14.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Macron zai kawo sauyi a Tarayyar Turai

Emmanuel Macron da ya sha rantsuwar kasancewa shugaban Faransa mafi kankancin shekaru, ya yi alkawarin kawo sauyi a kungiyar Tarayyar Turai.

Anasarn Macron zai tabbatar da goyon bayansa ba wai ga kungiyar ta EU kadai ba, har ma da Tarayyar Jamus, a lokacin ganawarsa da shugabar gwamnati Angela Merkel a ziyarar farko da zai kawo Berlin a gobe.

Kazalika a wannan Litinin din ce ake saran mai shekaru 39 da haihuwar, kuma tsohon ministan tattalin na Faransa, zai gabatar da sunan fraiministansa, a cewar majiya mai tushe da ke kusa da fadar shugaban kasar.

Kafofin yada labarun Faransan dai sun ruwaito rade-radin yiwuwar nada magajin garin Le Havre mai ra'ayin mazan jiya Edouard Philippe a matsayin sabon fraiministan, sai dai zaben 'yan majalisar wakilai da zai gudana a wata mai zuwa zai iya sauya komai, tunda wajibi ne jam'iyyar da ta fi rinjayen kujeru ta kasance mai kafa gwamnati.