1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya yabi sojojin Faransa a waje

Yusuf Bala Nayaya
December 23, 2018

Shugaba Emmanuel Macron da yake jawabi ga sojoji 1000 a birnin N'Djamena ya ce duk inda Faransa ke yakar 'yan ta'adda kare kanta take yi.

https://p.dw.com/p/3AZDU
Niger - Macrons Truppenbesuch
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya gana da dakarun kasar ta Faransa a kasar Chadi inda ya yaba masu kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin.

Da yake jawabi ga sojoji 1000 a birnin N'Djamena ya ce duk inda Faransa ke yakar 'yan ta'adda kare kanta take domin irisu ne suka kai hari a birnin Strasbourg.

Faransa dai na da dakarun soja 4,500 wadanda ke aiki cikin rundiyar Barkhane masu yakar 'yan ta'adda a Chadi da Mali da Burkina Faso da Mauritaniya da Mali da Nijar.