Mace-mace a hanyar coci a Omoku na Rivers | Labarai | DW | 01.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace-mace a hanyar coci a Omoku na Rivers

Mutane 35 sun mutu a jihar Rivers ta kudancin Najeriya a bukukuwan shiga sabuwar shekara ta 2018: Sai dai 'yan sanda na bincike don gano wadanda suka halakasu.

Wasu yan binduga da har yanzu ba a Kai ga ganosu ba a garin Omoku da ke jihar Rivers sun bude wuta irin na kan mai uwa da Wabi kan wasu dandazon Jama'a da suka hada da maza da mata har da kananan yara, inda kawo yanzu aka tabbatar da mutuwar mutane 35.

Wadanda suka rasa rayukannasu dai, suna dawowa ne daga taron ibada da kuma bikin Cross Over Night,wato taron tsallakawa daga shekara ta 2017 Zuwa 2018, da ya gudana a Coci Coci daban-daban a garin na omoku.

Har kawo yanzu dai, rundunar 'yan sandan jihar ta Rivers ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin kafin ta yi cikakken bayani kan zahairin abin da a afku.