London: Bukin cika shekaru 70 na NATO | Labarai | DW | 03.12.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

London: Bukin cika shekaru 70 na NATO

Kasafin kudin tafiyar ta NATO da rawar da rundunar kungiyar tsaron ke takawa a Afganinsatan, na daga cikin batutuwa da taron da ke gudana a birnin London zai mayar da hakali a kansu.

Sai dai kuma a wani abun da zai zama tamkar gwaji ne ga shugabannin kasashe 29 mambobin kungiyar ta NATO, yayin wannan zaman za su tattauna yadda huldarsu da Rasha makomarta zai kasance, da kuma duba tasirin kasar a harkokin tsaron duniya.

Duk da wannan batu na Rasha, shugabannin kungiyar tuni suka hallara a birnin London don bikin cikar kungiyar shekaru 70 da kafuwa. Babban abin da zai kankane taron ana saran ya zama batun kasafin kudin tafiyar da kungiyar.

Batun rundunar NATO a Afganistan shi ma na daga cikin abin da kan iya zama muhawara mai zafi, yayinda kasar Jamus ke kokarin ganin an tsawaita wa'adin dakarun NATO a Kabul, Amirka kuwa na cewa shiri ya kamalla na fidda sojojinta daga Afganistan.