1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta amince da bukatar Nnamdi Kanu

Abdul-raheem Hassan
December 2, 2021

Babbar kotun Tarayya da ke sauraraon shari'ar Shugaban Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu a Abuja, ta saurari korafin lauyoyinsa da ke zargin ba a ba shi kulawa yadda ya kamata.

https://p.dw.com/p/43lAE
Politischer Aktivist IPOB Nwannekaenyi Nnamdi Kenny Okwu Kanu im Gerichtssaal in Abuja
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Lauyoyin da ke kare shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu sun bukaci kotun da ke sauraron shari'ar a Abuja, ta umarci hukumar tsaron farin kaya bai wa Kanu din damar walwalar ganawa da mutane da abinci mai kyau tare gudanar da ibada.

Yanzu haka dai kotu ta sake dage shari'ar da ake wa Nnamdi Kanu zuwa watan Janairu na shekarar 2022, inda gwamnatin Najeriya ke zarginsa da laifuka bakwai ciki har da ta'addanci da cin amanar kasa.